Isa ga babban shafi
India-Pakistan

Pakistan ta dage haramcin haska fina-finan India

Manyan Gidajen haska fina-finai a kasar Pakistan sun amince da kawo karshen matakin haramta haska fina-finan India a kasar, wanda suka dauka a watan Satumba.

Fina-finan masana'antar Bollywood
Fina-finan masana'antar Bollywood
Talla

A baya dai an dauki matakin haramta haska fina-finan a Pakistan, sakamakon tabarbarewar dagantakar kasashen biyu, bisa yankin Kashmir da suka jima suna takaddama a kansa.

Da fari dai masu shirya Fina Finan kasar India ne, suka fara daukar matakin harmatawa jaruman da suka fito daga kasar Pakistan haskawa cikin fina-finansu, sakamakon haka a Pakistan, aka haramta haska fina finan indian, matakan da suka haifar da hasarar dimbin kudaden shiga ga bangarorin biyu.

Pakistan ta taba haramta a fina finan India a shekarar 1965 a lokacin da aka gwabza yaki tsakanin kasashen biyu inda sai a shekara ta 2008 ta dage haramcin a hukumance.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.