Isa ga babban shafi
Syria

Sojin Syria sun kaddamar da sabon farmaki kan 'yan tawaye

Sojin Syria sun kaddamar da sabon farmaki kan mayakan ‘yan tawaye da ke wasu kauyuka a wajen birnin Aleppo. 

Zubar dusar kankara mai yawan gaske a sassan kasar Syria na dakile ayyukan bada agaji
Zubar dusar kankara mai yawan gaske a sassan kasar Syria na dakile ayyukan bada agaji REUTERS/Abdalrhman Ismail
Talla

Matakin na zuwa ne bayanda wata kafar talabijin din Syrian ta bada rahoton cewa akalla mutane 3 suka rasa ransu sakamakon harin da wasu ‘yan tawaye suka kai a wasu kauyuka da ke wajen Aleppo, wanda sojin Syria sukai nasarar kame shi.

A gafe guda kuma kungiyar kare hakkin dan’adam da ke kasar ta Syria, ta ce fararen hula 6 suka mutu sakamakon barin wutar da jiragen yaki sukai a garin Atareb da ke yamma da Aleppo, kuma ana zaton jiragen rasha da Syria ne suka kai harin.

Rahotanni sun ce jiragen yakin sun fi maida hankali kan barin wutar a gabashi, kudanci da kuma arewacin yankunan da ke wajen birnin Aleppo.

Ana cigaba da bayyana fargaba kan halin da fararen hula da ke kauyukan wajen birnin Aleppo, wadanda har yanzu basu samu damar ficewa daga yankunan ba.

A gafe guda jami’an agaji sun ce zubar dusar kankara mai yawan gaske ya sanya ayyukansu na kai agaji ga sassan Syria wahala, inda rohotanni suka ce wasu fararen hula ciki harda mata da kanan yara sun rasa ransu sakamakon tsanin sanyi a sassan kasar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.