Isa ga babban shafi
Syria

An amince da shirin tura jami’an sa ido zuwa birnin Aleppo

Majalisar  Dinkin Duniya ta sanar da shirin tura jami’an sa ido 20 zuwa birnin Aleppo dan ganewa idan su halin da ake ciki da kuma yadda ake kwashe fararen hula tare da tabbatar da adalci.

Majalisar Dinkin Duniya  za ta tura jami’an sa ido birnin Aleppo.
Majalisar Dinkin Duniya za ta tura jami’an sa ido birnin Aleppo.
Talla

Kakakin Majalisar Stephaine Dujjaric ya ce tuni gwamnatin Syria ta amince da shirin tura jami’an kwana guda bayan kwamitin Sulhu na Majalisar ya amince da shirin.

Akalla mutane 25,000 aka kwashe daga Gabashin birnin kamar yadda kungiyar agaji ta Red Cross ta sanar.

Gwamnatin Syria ta bukaci 'Yan Tawayen da suka rage da su gaggauta ficewa daga Yankin.

Kwamitin Sulhu ya dauki wannan mataki ne na tura masu sa ido Aleppo dan ganin halin da ake ciki musamman zargin musugunawa fararen hular da ake yiwa Gwamnatin Syria.

Dubban fararen hula ne ke ci gaba da ficewa daga birnin Aleppo dake  a ci gaba da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka kulla wadda ake ganin za ta bai wa gwamnati Bashar al Assad ci gaba da iko da birnin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.