Isa ga babban shafi
Iraqi

Majalisar Iraqi ta bukaci gwamnati ta maidawa Amurka martani

Majalisar Iraqi ta bukaci gwamnatin kasar ta maida martini kan matakin da Donald Trump ya dauka, na haramtawa ‘yan kasar da wasu na kasashen Musulmi 6 shiga Amurka.

Zauren Majalisar kasar Iraqi
Zauren Majalisar kasar Iraqi
Talla

A ranar Litinin, Majalisar kasar ta kada kuri’ar amincewa da kudurin bawa gwamnatin kasar ta Iraqi goyon bayan maida martini kan matakin da sabon shugaban na Amurkan.

A ranar Litinin din data gabata Trump ya sanya hannu kan dokar dakatar da shigar musulmi da kuma baki Amurka, lamarin da ya shafi manyan kasashen Musulmi 7 ciki harda Iraqi, wadda Amurka ta girke sojinta 5000 don yakar mayakan IS.

Wannan mataki na sabon shugaban Amurka Donald Trump na cigaba da fusata jama’a a sassan duniya, inda aka shiga rana ta biyu anagudanar da zanga zangar adawa da dokar biranen Amurka, ciki harda biranen Washington da New York.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.