Isa ga babban shafi
Iraqi

Dakarun Iraqi sun yi ikirarin kwato gabashin Mosul

Dakarun Iraqi sun sanar da kakkabe mayakan IS daga gabashin Mosul baki daya, inda yanzu rabin birnin ya dawo karkashin gwamnatin kasar. Laftanar Talib Shaghati da ke jagoranta sojojin da ke yaki a Mosul, ya ce nan da lokaci kankani za su kwato sauran yankunan garin.

Dakarun Iraqi sun yaki IS a gabashin Mosul
Dakarun Iraqi sun yaki IS a gabashin Mosul REUTERS/Ahmed Saad
Talla

Dakarun Iraqi sun ce yankunan Mosul kadan suka rage a kakkabe IS.

A cewar Laftanar Talib Shaghati wanda ke jagoranta rundunar da ke yakar IS, sun yi farin ciki matuka da ganin babu sauran mayakan na jihadi a gabashin kasar.

Dakarun Iraqi na samun taimakon dakarun kawance Amurka ga yakin da suke na tarwatsa IS a Mosul.

Friministan Iraqi Haidar al-Abadi ya ce saura kiris su yi nasara kan Mayakan kuma tuni aka karya lagon IS.

An dai kwashe sama da watanni Uku ana dakarun Iraqi na fada da IS a birnin da ya kasance na karshe da mayakn ke da karfi a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.