Isa ga babban shafi
Isra`ila-Iran

Netanyahu ya bukaci kasashen duniya su goyi bayan ladabtar da Iran

Firaministan Isra’ila da ke ziyara a Birtaniya, Benjamin Netanyahu ya bukaci manyan kasashen duniya da su goyi bayan sabbin takun-kuman karayar tattalin arziki da aka sake kakabawa kasar Iran.

Firaministan Isra`ila Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra`ila Benyamin Netanyahu REUTERS/Abir Sultan
Talla

A yayin ganawa da takwararsa ta Birtaniya Theresa May a birnin London, Mr. Netanyahu ya bayyana jin dadinsa gameda turjiyar da shugaban Amurka Donald Trump ya nuna don ganin an sanyawa kasar ta Iran sabbin takunkuman.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya kuma soki tare da zarginta da tada da zaune tsaye sakamakon gwajin makami mai linzami da ta yi, yayin da ya bukaci manyan kasashen duniya da su goyi bayan matakan ladabtarwa da aka dauka akanta.

Netanyahu ya kuma zargi, Iran da shirin ruguza Isra’ila tare da ribatar yankin gabas ta tsakiya, baya ga barazanar da take yi wa Turai da kuma daukacin duniya baki daya.

A makon jiya ne shugaban Amurka Donald Trump ya ce, a yanzu sun sanya ido kan Iran a hukumannce bayan gwajin makami mai linzami da ta yi.

Zalika Mr. Trump ya nuna adawa da yarjejeniyar Nukiliya da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya.

A nata bangaren, Iran ta dage kan cewa, gwajin makamin na linzami da ta yi, bai sabawa ka`idar yarjejeniyar da aka cimma da ita ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.