Isa ga babban shafi
Syria

Ana amfani da makamai masu guba a Aleppo-HRW

Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Human Right Watch ta ce Sojojin Gwamnatin Syria sun yi amfani da makamai masu guba makonnin karshe na yakin da aka yi a Aleppo inda aka kashe mutane tara da suka hada da yara kananan hudu.

Birnin Aleppo da ke Syria ya fuskanci munanan hare-hare
Birnin Aleppo da ke Syria ya fuskanci munanan hare-hare KARAM AL-MASRI / AFP
Talla

A cewar wani rahoto da ta fitar, kungiyar ta ce ta tattauna da ganau, kuma akwai ta da hotuna da bidiyo da ke nuna an yi amfani da Bama-bamai da ke kunshe da sinadarin Chlorine da jiragen gwamnati masu saukan ungulu a ranakun 17 ga watan Nuwamba da 13 ga watan Disamba na shekarar da ta gabata.

Kungiyar ta ce mutane kusan 200 suka jikkata sakamakon amfanin da guban.

Wannan adadi, inji kungiyar na iya zarce haka, domin akwai wasu bayanai daga ‘yan jaridu, masu aikin asibiti da wasu majiyoyi masu tushe da ke nuna sau 12 ana kai hare-haren da guba.

Wannan rahoto ya bayyana munin hare-haren a filayen wasanni, gidajen jama’a, dakunan shan magani da wasu muhimman wurare, inda aka bar mutane na fama da matsaloli wajen shakar iska da amai da suma.

A Bayanin dai babu alamar akwai hannun kasar Rasha a wannan hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.