Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada matsayinta kan siyasar Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta jaddda cewa zaman tattaunawa kan rikicin kasar Syria da za’yi a Geneva zai maida hankali ne kan warware dambarwar siyasar kasar.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria Staffan de Mistura yayin gabatar da wani jawabi a birnin Rome
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria Staffan de Mistura yayin gabatar da wani jawabi a birnin Rome timesofoman
Talla

Hakan na zuwa, dai dai lokacin da wasu ke fargabar, majalisar dinkin duniyar na kokarin janyewa daga matsayinta, na jagorantar warware rikicin siyasar kasar da za’a tattauna a kai a ranar Alhamis.

Ofishin jakadan musamman na majalisar dinkin duniya a Syria Staffan de Mistura ne ya musanta rade radin, tare da tabbatar da cewa babbar manufar taron har yanzu na kan batun warware rikicin siyasar kasar.

Yayin tarukan sulhu tsakanin ‘yan adawar Syria da gwamnati a baya, batun saukar shugaban kasar Bashar al-Assad ke mamaye tattaunawar, bukatar da har gwamnatin Assad ke cigaba da yin watsi da ita.

To sai dai kuma, mai yiwuwa ne bangaren ‘yan adawar na Syria su jingine bukatarsu idan aka yi la’akari da janye goyon bayan bukatar tasu da kasashen Amurka da Turkiya suka yi, wadanda suka yi na’am da bukatar baya.

Kakakin ofishin jakadan majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria, Micheal Contet, ya ce taron na ranar Alhamis zai maida hankali ne kan yadda za’a kafa gwamnatin rikon kwarya, samar da sabon kundin tsarin mulkin kasa, sai kuma gudanar da sahihin zabe a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.