Isa ga babban shafi
Syria

Tattaunawa kan rikicin Syria a Geneva

Jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Syria Staffan de Mistura ya bukaci wakilan gwamnati da na ‘yan adawa dake halartar taron sasanta rikicin kasar a Geneva, da su yiwa Allah su dauki matakin kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 6 ana fafatawa.

Jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Syria Staffan de Mistura
Jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Syria Staffan de Mistura REUTERS/Denis Balibouse
Talla

De Mistura yace lokaci yayi da wakilan dake halartar taron zasu dauki matakin da zai kare yaran kasar da kuma kawo karshen zubar da jinin da akeyi.

Akalla mutane sama da 400,000 aka kashe a yakin da ake ci gaba da fafatawa a kasar, yayin da kowanne bangare ke dagewa sai ya samu biyan bukata.

‘Yan adawar Syria dai na bukatar ganin shugaban kasar Bashar al-Assad ya sauka daga mukaminsa ya bawa gwamnatin wucin gadi da za’a kafa ragamar jagorantar kasar, bukatar da gwamnatin Assad ta yi watsi da ita, yayinda a gefe guda kuma Amurka da Turkiya suka janye daga goyon bayan bukatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.