Isa ga babban shafi
Cambodia-Amurka

Cambodia ta dakatar da cinikin ruwan nonon mata da Amurka

Kasar Cambodia ta dakatar da safarar ruwan nonon matan da ake yi tsakanin kasar ta zuwa Amurka sakamakon rashin samun izini daga gwamnatin kasar.

Ruwan nonon  da aka  tatse aka kuma sanya shi cikin na’urar dake mayar da shi kankara
Ruwan nonon da aka tatse aka kuma sanya shi cikin na’urar dake mayar da shi kankara RFI/Alice MILOT
Talla

Hukumar kwastam dake kasar Cambodia ta sanar da dakatar da safarar ruwan nonon matan da wani kamfanin Amurka Ambrosia Labs keyi, wanda shine irin sa na farko a duniya, inda ake sayen ruwan nonon mata daga kasar ana kaiwa Amurka dan sayarwa matan da basa iya samar da nonon ko kuma basa samar da isashe da zasu baiwa jira jiran su.

Shi dai ruwan nonon akan tatse shi ne a Cambodia, kana a sanya shi cikin na’urar dake mayar da shi kankara kafin a dauke shi zuwa Amurka, kuma ana sayar da gram 147 akan kudi Dala 20.

Darakta Janar na hukumar kwastam dake Cambodia Kun Nhem yace sun bukaci kamfanin ya tattauna da ma’aikatar lafiyar kasar dan samun izini.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.