Isa ga babban shafi
Syria

Bankin Duniya ya fitar da alkalumman hasarar da Syria ta tafka

Wani rahoton Bankin Duniya ya ce kasar Syria ta tafka hasarar dala biliyan 226 na tattalin arzikinta, sakamakon yakin basasar da aka shafe shekaru 6 ana gwabzawa a kasar, wanda ya tagayyara al’ummarta.

Yankin arewacin garin al-Baab na Syria, da yaki ya ruguza.
Yankin arewacin garin al-Baab na Syria, da yaki ya ruguza. REUTERS/Khalil Ashawi
Talla

Rahotan ya kuma ce an samu salwantar gine-gine da hasarar rayuka dubu 320, bayan rabin al’ummar kasar da ke gudun hijira.

Mataimakin shugaban Bankin Duniya reshen gabas ta tsakiya da arewacin Afrika, Hafez Ghanem, ya ce yakin Syria ya tarwatsa duk wani abin ci gaba da tattalin arzikin kasar.

Hafez ya ce babu shakka alkalluman rayukan da aka salwantar abin damuwa ne, kuma yakin ya tarwatsa duk wani abu da kowacce al’umma ke bukata don wanzuwa, tare da haifar da babban kalubale kafin samun nasarar sake gina kasar.

Rahotan ya kara da cewa, tun bayan fara yakin Syria, zuwa yanzu, an tafka hasarar kashi 27 cikin 100, na gidaje, cibiyoyin samar da lafiya da ilimi da ke kasar.

Rahotan ya kuma yi hasashen cewa, da za’a kawo karshen yakin Syria a yau, ma’aunin tattalin arzikin kasar zai daga da kashi 41 cikin 100 cikin shekaru 4 masu zuwa, amma akasin haka zai ci gaba da durkusar da tattalin arzikinta a kowacce shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.