Kasashen ASEAN na taro kan tsaro a Manila
A yayin da kasashen kasashen yankin yamma maso gabashin nahiyar Asiya, ASEAN suka fara taro a birnin Manila na Philippines kan sha'anin tsaro, kasar Vietnam ta bukaci takwarorinta da su dauki tsattsauran mataki kan yadda China ke ci gaba da mamaye tekun yammacin Sin.
Wallafawa ranar:
Vietnam ta bayyana haka ne a yayin da Ministocin Harkokin Wajen kasashen suka fara tattaunawa kan sha’anin tsaro da kuma shirin mallakar makami mai linzami na Korea Ta Arewa.
A gobe Lahadi ne ake saran manyan jami’an diflomasiyar China da Amurka da Rasha da Koriya ta Arewa za su halarci taron.
Taron na zuwa ne a yayin da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke shirin kada kuri’a kan kudirin da Amurka ta gabatar don tsananta takunkumi kan Korea ta Arewa bisa gwaje-gwajenta na makami linzami.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu