Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa

Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya Na Taro Game Da Karin Takunkumi Kan Korea ta Arewa

Komitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na jefa kuri'a  yau Asabar game da daftarin kudirin sabon takunkumi da Amurka ta gabatar domin kara kakabawa kasar Korea ta Arewa takunkumin kara karairaya ta.

Wani makami mai linzami da Korea ta Arewa ta yi gwaji mai suna  Hwasong-14 a ranar 4 ga watan Yuli.
Wani makami mai linzami da Korea ta Arewa ta yi gwaji mai suna Hwasong-14 a ranar 4 ga watan Yuli. RFI
Talla

Yau Asabar  ake sa ran a jefa kuri'ar amincewa ko kuma akasin haka a taron komitin sulhun.

Sabon takunkumin nada shirin ganin Korea ta Arewa ta yi hasarar kudaden da suka kai Dalan Amurka Biliyan daya na kudaden shigan ta.

A dan tsakanin nan dai Korea ta Arewa ta sha gwajin makamai masu hatsari duk da cewa manyan kasashen duniya sun sha hana ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.