Isa ga babban shafi
Iraqi

Dakarun Iraqi sun kori IS a Tal Afar

Dakarun Iraqi sun sanar da kwato tsakiyar garin Tal Afar mai yawan mabiya Shi’a bayan sun fatattaki mayakan IS da suka kwace ikon garin.

Dakarun Iraqi da ke yaki da IS a Tal Afar
Dakarun Iraqi da ke yaki da IS a Tal Afar MOHAMED EL-SHAHED/AFP
Talla

Dakarun na Iraqi sun ce sun kwace ikon tsaron ganuwar garin Tal Afar, kuma kafin ranar Sallah za su sanar da kwace garin baki daya.

A ranar lahadin makon jiya ne dakarun Iraqi tare da taimakon hare haren jiragen kawance da Amurka ke jagoranta suka kaddamar da farmakin kwato garin wanda ke tsakanin Mosul da kuma yankunan Syria da IS ke iko.

Ikirarin kwato Tal Afar na zuwa bayan gwamnatin Iraqi ta kwato Mosul a watan Yuli daga hannun mayakan na IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.