Isa ga babban shafi
Myanmar

Sama da 'yan kabilar Rohingya 400 aka hallaka a Myanmar

Kimanin mutane 400 aka kashe akasarinsu ‘yan Rohingya a rikicin da ya barke a jihar Rakhine da ke Myanmar kamar yadda ofishin babban hafsan sojin kasar ya sanar a yau Juma’a.

Wasu 'yan kabilar Rohingya da suka tserewa rikici yayinda suka tafiya cikin ruwa, bayan ketara kan iyakar Myanmar da Bangladesh-Myanmar, ranar 1 ga Satumban 2017.
Wasu 'yan kabilar Rohingya da suka tserewa rikici yayinda suka tafiya cikin ruwa, bayan ketara kan iyakar Myanmar da Bangladesh-Myanmar, ranar 1 ga Satumban 2017. REUTERS/Mohammad Ponir Hossain
Talla

Wata sanarwa da ofishin ya fitar ta ce, har izuwa ranar 30 ga watan Agustan da ya gabata, an kashe mutane Rohingya 370, yayinda jami’an tsaro 15 da kuma fararen hula 14 suka rasa rayukansu a cikin rikicin kwanaki takwas.

Babban Hafsan sojin kasar Min Aung ya kara da cewa zuwa yanzu sojin na Myanmar sun kame ‘yan tawayen kabilar Rohingya 9, yayinda suka samu gawarwakin wasu daruruwa.

Sai dai kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam na cewa, yawan ‘yan kabilar ta Rohingya da sojin kasar ta Myanmar suka yiwa kisan gilla ya zarta 400 kamar yadda ake bayyanawa, kasan cewar akwai rahotannin aikata kisan kiyashi ta hanyar bude wuta kan fararen hula ciki har da kananan yara a kauyen Chut Pyin, inda suka kwashe kimanin sa’o’i biyar suna tafka ta’asar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.