Isa ga babban shafi
Myanmar

Dubban 'yan kabilar Rohingya na fama da yunwa a Myanmar

Kungiyar agaji ta Red Cross, ta tura karin jami’anta zuwa arewa maso yammacin kasar Myanmar, inda al’amura suka yamutse, sakamakon barkewar sabon ricikin da ya tilastawa dubban ‘yan kabilar Rohingya tserewa daga kasar.

Wasu 'yan gudun hijira 'yan kabilar Rohingya, yayinda suke ketara wani kogi domin isa sansanin wucin gadi da suka kafa a kan iyakar Bangladesh-Myanmar.
Wasu 'yan gudun hijira 'yan kabilar Rohingya, yayinda suke ketara wani kogi domin isa sansanin wucin gadi da suka kafa a kan iyakar Bangladesh-Myanmar. REUTERS/Danish Siddiqui
Talla

Matakin kungiyar ta Red Cross ya zo ne, bayanda majalisar dinkin duniya, ta janye jami’anta daga jihar Rakhine, sakamakon zarginta da gwamnatin Myanmar ta yi, cewa tana goyon bayan ‘yan tada kayar baya na kabilar Rohingya.

A halin da ake ciki, jami’an agajin na Red Cross sun ce, yayinda hankalin kasashen duniya, ya koma kan Musulmi ‘yan kabilar Rohingya sama da dubu 290,000 da suka tsere zuwa Bangladesh, kwai wasu dubban ‘yan Kabilar da suka shafe sama da makwanni biyu a jihar ta Rakhine ba tare da sun samu abinci ba.

Gwamnatin kasar na cigaba da kare kanta da cewa, sojojinta na kokarin murkushe 'yan tawayen kabilar Rohingya ne, da suke kaiwa jami'an tsaron hare-hare.

Ko a makon da ya gabata, shugabar gwamnatin kasar ta Myanmar, Aung San Suu Kyi ta musanta cewa sojin kasar suna cin zarafin Musulmin 'yan kabilar Rohingya, ta hanyar yi musu kisan gilla da kuma kone musu gidaje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.