Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Amurka zata dandana kudarta - Korea ta Arewa

Korea ta Arewa, ta ce Amurka zata dandana kudarta, sakamakon jagorantar zartar da matakin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, na kakaba mata sabbin takunkuman karya tattalin arziki.

Shugaban Korea ta Arewa yayin bikin karrama masana kimiyyar kasar da suka taimaka wajen kera makamin nukiliya mai dauke da sinadarin Hydrogen. Wannan hoton dai kamfanin dillancin labaran Korea ta Arewa (KCNA) ne ya fitar da shi a ranar 10 ga Satumba, 2017.
Shugaban Korea ta Arewa yayin bikin karrama masana kimiyyar kasar da suka taimaka wajen kera makamin nukiliya mai dauke da sinadarin Hydrogen. Wannan hoton dai kamfanin dillancin labaran Korea ta Arewa (KCNA) ne ya fitar da shi a ranar 10 ga Satumba, 2017. Reuters
Talla

Zalika manyan ami’an Korea ta Arewan sun ce a kowane lokaci suna iya sake gwajin wani makamin nukilyar, bayan nasarar da suka samu dari bisa dari a gwajin da suka yi a ranar 3 ga watan Satumba na makamin nukiliyar mai dauke da sinadarin Hydrogen.

Amurka na son kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya haramtawa cinikayyar danyen mai da Korea ta Arewa, da kuma sanyawa shugaban Korea ta Arewan Kim Jong Un takunkumin tafiye-tafiye.

A farkon makon da muke, shugaba Kim Jong-Un ya gudanar da wani gagarumin bikin cin abinci domin karrrama masana kimiyar kasar, wadanda suka taimakawa kasar kera makamin nukiliyar da aka gwada makon jiya.

Kamfanin dillancin labaran kasar yace shugaban ya gudanar da bikin ne tare da manyan hafsoshin sojin kasar, inda aka yi raye raye da daukar hoto tare da shugaban.

Hotan da aka nuna na bikin na dauke da shugaba Jong-Un tare da wasu masana kimiyar kasar guda biyu Ri Hong Sop, na Cibiyar kera nukiliyar kasar da kuma Hong Sung Mu, mataimakin daraktan Jam’iyyar dake mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.