Isa ga babban shafi

Indonesia: Sama da mutane dubu 57 sun tsere daga gidajensu

Akalla Mutane sama da 57,000 suka tserewa gidajen su daga tsibirin Bali dake kasar Indonesia domin kaucewa aman wutar da wani tsauni keyi.

Hoton wani katafaren tsauni da ke garin Pucon a kasar Chile, yayinda yake aman wuta da narkakken dutse.
Hoton wani katafaren tsauni da ke garin Pucon a kasar Chile, yayinda yake aman wuta da narkakken dutse. Reuters
Talla

Rahotanni sun ce tsaunin Agung, dake da nisan kilomita 75 daga wurin shakatawar Kuta, ya fara tumbatsa ne tun a watan Agusta da ya gabata, kuma rabonsa da yin haka tun shekarar 1963.

Kakakin ma’aikatar agajin gaggawa Sutopo Nugroho yace akwai alamu mai karfi dake nuna cewar za’a samu aman wutar, wanda kuma shi ne dalilin da ya sa aka kwashe mazauna yankin zuwa wasu sansanoni domin kare lafiyar su.

Akalla mutane dubu daya ne suka rasa rayukansu sakamakon aman wuta da kuma narkakken dutse da tsaunin na Agung yayi a shekarar 1963.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.