Isa ga babban shafi
Jamus

Jamus ta kaddamar shirin kwashe mazauna Frankfurt 60,000

Jami’an agaji a Jamus, sun fara kwashe marasa lafiya daga asibitocin da ke birnin Frankfurt, a dai dai lokacin da ake shirin kwance wani shirge-gen bam da aka gano binne a wani sashi na birnin binne, wanda aka jefa tun lokacin yakin duniya na biyu.

Wani bam da bai fashe ba da aka gano a birnin Frankfurt ba Jamus, da ak jefa shi a lokacin yakin duniya na biyu.
Wani bam da bai fashe ba da aka gano a birnin Frankfurt ba Jamus, da ak jefa shi a lokacin yakin duniya na biyu. REUTERS/Ralph Orlowski
Talla

Zalika a yau din ne, ake sa ran kammala kwashe mazauna yankin akalla dubu 60,000, a wani yanayi da ba’a kara ganin irinsa ba tun bayan yakin duniya na biyu.

Ana kyautata zaton cewa, jitagen yakin Birtaniya ne suka jefa Bam din kirar HC 4000, yayin gwabza yaki da gwamnatin Nazi a lokacin yakin duniya na biyu, tsakanin shekarun 1939 zuwa 1945.

An gano bam din ne yayin aikin sabunta ginin wani sashin jami'ar da ke birnin na Frankfurt.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.