Isa ga babban shafi
Jamus

Jami'ai a Jamus sun ce tilas a kwashe mazauna Frankfurt 60,000

Jami’an tsaro a birnin Frankfurt na Jamus, sun yi gargadin cewa dole ne sama da mutane dubu 50,000 su kauracewa gidajensu, domin bai wa kwararru damar kwance wani shirgegen bam da aka gano binne a wani sashi na birnin, wanda aka jefa shi tun a lokacin yakin duniya na biyu.

Shirgegen bam din da aka jefa a birnin Frankfurt na Jamus a lokacin yakin duniya na biyu, ranar 1 ga Satumba, 2017..
Shirgegen bam din da aka jefa a birnin Frankfurt na Jamus a lokacin yakin duniya na biyu, ranar 1 ga Satumba, 2017.. REUTERS/Ralph Orlowski
Talla

Shugaban jami’an kashe gobarar birnin na Frankfurt Reinhard Ries, ya ce tarwatsewar bam din zai iya ruguza gari guda, kasancewar yana kunshe da wasu abubuwan fashewar da nauyinsu ya zarta ton daya da digo hudu (1.4).

Tuni dai shirye –shirye suka yi nisa domin kwashe mazauna birnin na Franfurt akalla dubu 60,000, domin kwance bam din da Birtaniya ta jefa a waccan lokacin na yakin duniya na biyu.

An gano bam din ne yayin aikin sabunta ginin wani sashin jami'ar da ke birnin na Frankfurt.

Kwashe mutanen dai shi ne mafi girman wanda aka taba gani a Jamus, domin kwance bama-baman da basu tashi ba, tun bayan kawo karshen yakin duniya na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.