Isa ga babban shafi
China

Ana amfani da jakuna wajen hada maganin gargajiya a China

Wani faifan bidiyo da kungiyar kare hakkin dabbobi, PETA, ta fitar ya nuna yadda wasu ‘yan kasar China a wasu gonakai, suke amfani da narkekiyar guduma wajen rusa kawunan jakuna, da nufin yin amfani da fatunsu wajen hada wani maganin gargajiya da suke kira ejiao.

Jakuna a wasu yankunan China
Jakuna a wasu yankunan China Education Images/UIG via Getty Images
Talla

Da dama daga cikin ‘yan kasar China, sun raja’a wajen amfani da maganin na ejiao, domin magance matsalar rashin zagayawar jinni a jiki, da kuma cutar rashin samun isashen barci.

Kungiyar kare hakkin dabbobin ta ce ta saki faifan bidiyon ne domin nunawa wadanda suke sayan maganin gargajiyar, yadda ake yi wa Jakuna akalla miliyan daya da dubu dari 8 kisan mugunta a kowace shekara domin hada musu maganin da suke bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.