Harin da Saudiyya ta kai a Yemen ya kashe mutane 14
Shaidun gani da ido sun ce harin da dakaru ƙarƙashin jagorancin Saudiyya suka kai a wata kasuwa da ke arewacin ƙasar Yemen ya kashe mutane 14.
Wallafawa ranar:
A cewar kamfanin dillancin labaru da ke ƙarƙashin yan tawayen ƙasar, harin wanda aka kai ta sama a yammacin Laraba ya kashe mutane 12, yayin da aka kai hari na daban kan wani gida a yankin Baqim, wanda ya kashe mutane 2.
Saudiyya na jagorantar dakarun ƙawance a Yemen tun cikin shekara ta 2015 a ƙokarin ta na dakatar da ƴan tawayen Huthi waɗanda suka ƙwace yankuna da dama a ƙasar.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce mutane 9,000 ne suka mutu a ƙasar ta Yemen tun lokacin da dakarun suka ƙaddamar da yaƙi da ƴan tawayen na Huthi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu