Isa ga babban shafi
Bangladesh

"Yawan 'yan kabilar Rohingya da ke gudun hijira ya zarta miliyan 1"

Gwamnatin Bangladesh ta ce zuwa yanzu ta kirga sama da ‘yan kabilar Rohingya da ke gudun hijira a sansanonin da ta kafa, wadanda ke kan iyakarta da kasar Myanmar.

Wasu 'yan gudun hijira, Musulmi 'yan kabilar Rohingya, yayin da suka kokarin karasawa sansanin da gwamnatin Bangladesh ta tanadar musu, bayan tsallaka kogin Naf da ke kan iyakar Bangladesh da Myanmar.
Wasu 'yan gudun hijira, Musulmi 'yan kabilar Rohingya, yayin da suka kokarin karasawa sansanin da gwamnatin Bangladesh ta tanadar musu, bayan tsallaka kogin Naf da ke kan iyakar Bangladesh da Myanmar. REUTERS/Adnan Abidi
Talla

Yawan ‘yan gudun hijirar ya zarta dubu 962, da Majalisar Dinkin Duniya ta ce sun tsere zuwa kudu maso gabashin kasar ta Bangladesh.

A karshen shekarar 2017 da ta gabata, rundunar sojin kasar Bangladesh, ta fara aikin kirga dubban masu gudun hijirar Musulmi ‘yan kabilar Rohingya da suka kwararo daga Myanmar, sakamakon cin zarafin da suke fuskanta daga sojin kasar a jihar Rakhine.

Aikin tantance yawan ‘yan gudun hijirar sharer fage ce ga fara mayar da su gida a mako mai kamawa, kamar yadda kasar ta Bangladesh ta cimma yarjejeniya da gwamnatin Myanmar, duk da cewa mafi akasarinsu sun kafe cewar ba zasu koma ba, sakamakon kisan gilla da azabtar da su da ake, baya ga yi wa matansu fyade.

Shugaban shirin rijistar Birgediya Janar Sa’idurRahman, ya zuwa yanzu ‘yan gudun hijira miliyan da dubu hudu, da dari bakwai da arba’in da biyu suka tantance, kuma har yanzu da akwai wasu dubban da ba’a kirga ba.

Akwai dai ‘yan gudun hijirar kabilar Rohingya masu yawan gaske da suka dade suna gudun hijira a kasar Bangladesh, sai dai shirin mayar da su zai shafi ‘yan gudun hijirar da suka kwarara cikin kasar ne daga watan Oktoban shekara ta 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.