Isa ga babban shafi

Kabul: Jami'an tsaro sun murkushe harin 'yan bindiga kan Otal

Ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar Afghanistan ta sanar da kawo karshen harin da wasu ‘yan bindiga uku suka kaddamar kan Intercontinental wani babban Otal da ke birnin Kabul.

Otal din Intercontinental da 'yan bindiga suka kai wa hari a birnin Kabul.
Otal din Intercontinental da 'yan bindiga suka kai wa hari a birnin Kabul. Reuters
Talla

Mutane shidda ‘yan bindigar suka hallaka tare da raunata da dama yayin harin, kafin daga bisani jami’an tsaro su hallaka baki dayan maharan 4, bayan shafe awanni 12 suna musayar wuta a cikin otal din mai hawa 6.

A daren jiya Asabar ‘yan bindigar suka kutsa kai cikin Otal din, inda suka bude wuta kan mutane tare da tarwatsa bama-baman gurneti, lamarin da ya haddasa tashin gobara a sassan ginin na otal din.

Ma'aikatar cikin gidan kasar ta Afghanistan ta ce jami'an tsaro sun yi nasarar kubutar da mutane 150 da suka kunshi 'yan kasashen ketare 40.

Har yanzu babu wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin, sai dai gwamnatin kasar ta dora alhakin kan kungiyar Taliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.