Isa ga babban shafi
Faransa-Iran

Faransa ta zargi Iran da baiwa mayakan Houthi makamai

Kasar Faransa ta zargi Iran da baiwa ‘yan tawayen Houthi na Yemen makamai da take amfani da su wajen yaki a kasar, da kuma kaiwa Saudi Arabia hari.

Wasu daga cikin mayakan Houthi na kasar Yemen.
Wasu daga cikin mayakan Houthi na kasar Yemen. REUTERS/FILE
Talla

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian, yace lallai akwai matsala a Yemen, inda har yanzu aka gaza shawo kan matsalar kasar ta fannin siyasa, yayin da ‘yan Tawayen Houthi ke amfani da makaman da suke samu daga Iran wajen kaiwa Saudiya hari.

Kasar Iran ta dade tana musanta cewar ita take baiwa ‘yan Tawayen makamai, sai dai ta bayyana goyon bayan gwagwarmayar da ‘yan tawayen ke yi.

A karshen makon da ya gabata ne saudiya ta yi barazanar ka iwa Iran hari biyo bayan harin makamai masu linzami guda 7 da mayakan Houthi suka kai kan birnin Riyadh, wanda ya yi sanadin hallakar mutum guda da raunata mutane 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.