‘Yan tawayen Huthi lashi takobin cigaba da gwabza fada da dakarun kawancen
Yan tawayen Huthi a kasar Yemen sun lashi takobin cigaba da gwabza fada da dakarun kawancen kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya domin kare birnin Hodeida mai tashar jiragen ruwa.
Wallafawa ranar:
An dai share kusan kwanaki 6 ana gwabza fada tsakanin dakarun da kuma ‘yan tawayen a wannan birni mai mutane sama da dubu 600.
A wani bincike daga Majalisar Dinkin Duniya,hukumar ta gano cewa akwai akalla iyalai 5000, sun rasa muhallansu a Yemen, sakamakon hare-haren da dakarun kawance na Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya suka kaddamar, don kwace birnin Hodeida mai tashar jiraren ruwa daga ‘yan tawayen Houthi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu