Isa ga babban shafi
Korea

Iyalai a kasashen Koriya 2 sun gana bayan shekaru 65 da raba su da juna

Koke koke ihuce ihuce da dariya ne suka kaure a lokaci guda, a yau litanin a yayin da yan kasar koriya ta kudu yan uwa suka hada hannu tare da rungumar juna bayan da yakin shekarun (1950-1953), ya raba da juna.

Haduwar iyalan gida guda  da aka raba da juna a kasashen koriya ta kudu da ta arewa  20  ogusta 2018.
Haduwar iyalan gida guda da aka raba da juna a kasashen koriya ta kudu da ta arewa 20 ogusta 2018. Yonhap via REUTERS
Talla

Wannan sabuwar haduwa mai dimautarwa da tarihi, a taron tattaunawar da iyalan da aka raba, ita ce irin ta na farko a cikin shekaru 3, ana kuma gudanar da ita ne a yankin kan ikayar nan mai tsaunuka na Kumgang dake cikin kasar koriya ta arewa.

Haduwar dai wata babbar dama ce, ga yan uwa 2 da suka kasance masu yawan shekaru wajen yin masafaha tare da sumbatar juna, bayan da aka tilsata masu rayuwa rarrabe, sakamako shingen waya da kuma nakiyoyin da aka daddasa a tsakaninsu yau da shekaru 65 da suka gabata.

Quand Han Shin-ja, tsohuwa mai shekaru 99 yar Koriya ta kudu, ta hadu da ya yanta mata guda biyu, day yar shekaru 72 da kuma kanwarta mai shekaru 69, wadanda suka sunkuyar da kai kasa domin girmamawa ga mahaifiyar tasu kafin su shiga zubar da hawaye Han ganin yayan nata keda wuya ta fashe da kuka, kafin ta shiga murna tare da yanyanta mata guda biyu abin tausai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.