Isa ga babban shafi
Koriya ta Arewa-Korea ta Kudu

Ana sa ran ganawar iyalan da yakin Koriya ya raba

Kungiyar bayar da agaji ta Croix-Rouge ta bayyana cewa a yau juma a ne kasashen koriya ta kudu da ta arewa zasu gana domin tattauna sake komawa ganawar iyalan da yakin basasar kasashen na 1950-53 ya raba a yankin kan iyakokin da suka raba kasar.

Ministocin kasashen Koriya ta Arewa da na Koriya ta Kudu
Ministocin kasashen Koriya ta Arewa da na Koriya ta Kudu © Reuters
Talla

Miliyoyin mutane ne aka raba iyalansu sakamakon yakin kasashen yau da shekaru 70 ke nan da suka gabata .

Idan aka yi tuni kasar Korea ta Kudu ta fitar da wani tsarin tattaunawar sulhu da makwabciyarta Korea ta Arewa a ranar 9 ga wata na Janairu farkon shekarar nan.

Tattaunawar da ke biyo bayan tayin da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong-Un ya gabatar a jawabansa na shiga sabuwar shekara da ke cewa, kasar na bukatar halartan gasar wasannin Olypmics.

Kasashen biyu da basa ga maciji tun kawo karshan yakin koriya a shekara ta 1950 zuwa 1953, rabonsu da zaman tattaunawa tun a cikin shekara ta 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.