Isa ga babban shafi
India

Tarzomar addini ta tsananta a India

Sabuwar tarzoma ta barke tsakanin mabiya addinin Hindu da jami’an ‘yan sanda a jihar Kerala da ke yankin kudancin India bayan wasu mata biyu sun shiga cikin wani dakin bauta na Sabarimala, abin da ya saba wa al’adar yankin.

Jami'an 'yan sandan India cikin rakiyar matan da suka shiga dakin bautar Sabarimala
Jami'an 'yan sandan India cikin rakiyar matan da suka shiga dakin bautar Sabarimala REUTERS/Stringer
Talla

Tun a ranar Laraba aka fara tarzoma a jihar, yayin da mutun guda ya rasa ransa baya ga 15 da suka jikkata.

Haramun ne mace mai shekarun al’ada ta shiga cikin dakin bautar Sabarimala, amma wadannan mata biyu suka keta wannan ka’idar bayan kotu ta soke haramcin

Matan sanye da bakaken tufafi sun samu rakiyar jami’an ‘yan sanda kafin samun nasarar shiga cikin dakin, in da suka yi addu’o’i kafin bullowar alfijir.

A cikin watan Satumban da ya gabata ne, kotun kolin India ta soke al’adar haramta wa mata shiga dakin bautar, abin da ya bai wa matan kwarin guiwar shiga a yanzu.

Jam’iyyar Bharatiya Janata mai mulki ta goyi bayan zanga-zangar mabiya addinin Hindu a Kerala, yayin da da rundunar ‘yan sandan kasar ta dora alhakin mutuwar mutun guda kan jam’iyyar wadda ta rura wutar zanga-zangar.

‘Yan sanda na amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma ruwan zafi wajen tarwatsa dubban masu zanga-zangar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.