Isa ga babban shafi
India-pakistan

Pakistan da India sun yi ikirarin kakkabo jiragen yakin juna

Kasashen Pakistan da India sun yi ikirarin kakkabo jiragen yakin juna, a wani rikici da ke dada kamari tsakaninsu, kuma ake fargabar cewa za a samu fito na fito tsakanin kasashen makwabtan juna masu makaman nukiliya.

Yau Laraba ne dai kasashen biyu suka mayarwa juna martini ta hanyar jijjigo jiragen juna bayan harin makonnin baya-bayan nan da ya hallaka sojin India da dama
Yau Laraba ne dai kasashen biyu suka mayarwa juna martini ta hanyar jijjigo jiragen juna bayan harin makonnin baya-bayan nan da ya hallaka sojin India da dama REUTERS/Danish Ismail
Talla

kasashen biyu dai na kai ruwa rana ne kan yankin Kashmir da ke karkashin ikon India, lamarin da ya yi sanadiyar hassala rikicin da ke tsakaninsu a karon farko cikin shekaru 20.

Kakakin ma’aikatar tsaron India, Raveesh Kumar, a yau Laraba ya ce an fara zube-ban kwarya ne, bayan da sojin Pakistan suka fara kai hari kan sojin da India ta girke a yankin Kashmir.

A bangare guda Firaministan Pakistan, Imran Khan wanda ya nemi kasashen biyu su tattauna don samar da mafita, ya ce duk da haka Pakistan ba za ta tsaya ta na kallo ba, don kuwa za ta dauki matakan da suka dace don kare kanta.

Firaminista Imran Khan ya kuma bayyana yadda jiragen yakin India suka ratsa kasarsa ba tare da izini ba, matakin da ya tilasta su kakkabo jiragen tare da kame matukansu.

Rikicin ya tashi ne bayan wani harin bam da ya yi sanadin mutuwar dakarun India 40 a yankin Kashmir ranar 14 ga watan Fabarairu, hari mafi muni cikin shekaru 30 na rikicin tsakanin India da Pakistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.