Isa ga babban shafi
Vatican

Fafaroma ya bukaci masu sana'ar kitso da yankan farce su daina gulma

Shugaban mabiya darikar katolika na duniya, Fafaroma Francis ya bukaci masu kitso da yankan farce da su rage gulma ko tsegumi lokacin da su ke gudanar da sana'arsu.

Shugaban Mabiya darikar Katlika na duniya Fafaroma Francis
Shugaban Mabiya darikar Katlika na duniya Fafaroma Francis Vincenzo PINTO / AFP
Talla

Yayin karbar masu wannan sana’a da suka ziyarce shi a fadar Vatican, Fafaroman ya bukace su da su gudanar da ayyukansu kamar yadda addinin Kirista ya tanada ba tare da tsegumin da ke haifar da matsala ba.

Fafaroman ya shaida musu cewar kowa daga cikin su na da rawar da zai taka wajen inganta rayuwar al’umma.

A shekarar 2015 Fafaroma Francis ya bude shagon aski da wanka ga mutannen da basu da muhalli a Dandalin St Peters.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.