Isa ga babban shafi
Vatican

Fafaroma ya roki gafarar Ubangiji kan ta'asar Ireland

Shugaban Mabiya Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis ya roki gafarar Ubangiji kan badakalar cin zarafin yara kanana da ta mamaye mujami’ar Katolika a kasar Ireland.

Shugaban Katolika ta Duniya , Fafaroma Francis
Shugaban Katolika ta Duniya , Fafaroma Francis REUTERS/Dylan Martinez
Talla

Yayin da yake jawabi a gaban mabiyansa sama da 45,000 da ke tsaye a cikin ruwan sama, Fafaroman ya yi tsokaci kan illar da cin zarafin ya haifar da kuma bukatar daukar matakai masu tsauri domin tabbatar da gaskiya da kuma hukunci kan lamarin.

Sai dai Fafaroman ya ki cewa komai kan zargin sa da wani babban jami’in Fadar Vatican, Archbishop Carlo Maria Vigano ya yi na cewar ya kauda kansa daga zargin cin zarafin da ake yi wa Cardinal Theodore McCarrick na Amurka.

Archbishop Vigano ya ce, ya sanar da Fafaroman game da badakalar da ta dabaibaye Cardinal McCarrick a shekarar 2013 amma bai dauki mataki ba, hasali ma, ya yi gaban kansa wajen janye takunkuman da tsohon Fafaroma Benedict ya kakaba wa McCarrick.

A watan jiya ne, McCarrick ya yi murabus daga mukaminsa, yayin da Vigano ya bukaci Fafaroma Francis da shi ma ya yi murabus a wata wasika da ya rubuta masa a ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.