Isa ga babban shafi

Sojin Rasha da Syria sun wargaza yarjejeniyar tsagaita wuta a Idlib

Kawancen sojojin Rasha da na gwamnatin Syria sun ci gaba da barin wuta kan lardin Idlib da ke arewa maso yammacin kasar, bayan soke yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma da ‘yan tawayen kasar a watannin baya.

Wani yanki da Sojin Rasha suka farmaka a Idlib na Syria
Wani yanki da Sojin Rasha suka farmaka a Idlib na Syria © White Helmets/social media via REUTERS
Talla

Kawancen dakarun na Rasha da na gwamnatin Bashar Al – Assad sun soke yarjejeniyar tsagaita wutar ce, bayan zargin ‘yan tawayen Syria da kai farmaki kan wani sansanin sojin saman Rasha da ke kasar.

Yarjejeniyar tsagaita wutar ta rushe ne kwanaki uku kacal bayan soma aikinta cikin makon da ya gabata a ranar Juma’a.

An dai shafe akalla watanni uku ana gumurzu a lardin na Idlib, inda kawancen sojin Syria da Rasha suke barin wuta da nufin tumbuke ragowar mayakan ‘yan tawayen kasar da ke iko da yankin, lamarin da yayi sanadin halakar fararen hula sama da 700, wasu akalla dubu 400 kuma suka tserewa muhallansu.

Lardin Idlib da ke arewa maso yammacin Syria da akalla mutane miliyan 3 ke zaune, na daga cikin manyan yankunan da suka rage a karkashin ikon ‘yan tawayen da suka shafe shekaru 8 suna fafutukar kifar da gwamnatin Bashar Al- Assad.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.