Isa ga babban shafi
Japan-Lebanon

An gano dabarun da Ghosn ya yi wajen tserewa daga Japan

Wasu sabbin rahotanni a yau Litinin sun fayyace salon dubarun da tsohon shugaban kamfanin Nissan Carlos Ghosn ya yi amfani da su wajen tserewa shari’a a Japan, dai dai lokacin da ma’aikatar shari’ar ta Japan ke cewa ya zama wajibi a tuhumi ma’aikatar shige-da-ficenta don lalubo wadanda suka taimakawa jami’in tserewa zuwa Lebanon.

Tsohon shugaban hadakar kamfanin Nissan da Renault Carlos Ghosn.
Tsohon shugaban hadakar kamfanin Nissan da Renault Carlos Ghosn. REUTERS/Issei Kato/File Photo
Talla

Carlos Ghosn Bafaranshe mai shekaru 65 tun a makon jiya ne ya yi nasarar sulalewa daga Japan duk da matakan tsaron da aka gindaya masa da kuma sharuddan belinsa da bai sahale masa barin kasar ba, dai dai lokacin da ake yi masa daurin talala gabanin fara yi masa shari’a a wata mai zuwa, wasu rahotanni sun bayyana cewa Ghosn ya samu taimakon wasu mutane 2 da suka tallafa masa barin kasar.

Ko jawaban sashen tsaro na Japan a Litinin din nan, Japan ta bayyana cewa har yanzu bata gama gano yadda jami’in ya tsere ba, duk kuwa matakan tsaron da ta ke ikirarin samarwa a tsashoshinta na jiragen sama.

Wata majiya da ke da kusanci da Ghosn ta bayyana cewa tsohon shugaban na Nissan ya bar gidansa da kansa cikin yammacin ranar 29 ga watan Disamban bara inda ya hadu da wasu mutane 2 a Otel din birnin Tokyo inda daga bisani su 3 suka yi amfani da jirgin kasa daga tashar Shinagawa zuwa yammacin Osaka yankin da suka samu isa da misalin karfe 7 :30 na daren ranar.

Majiyar ta bayyana ko da bayan gano ficewar Ghosn da mutanen ta hanyar amfani da kyamarar tsaro, jami’an tsraon da suka yiwa dakin otel din da suka sauka a gab da filin jirgin saman Kansai mutanen 2 kadai suka yi nasarar kamewa yayinda Carlos Ghosn ya yi batan dabo.

Rahotanni dai sun bayyana cewa akwai yiwuwar Ghosn ya yi amfani da wani Fasfo na daban maimakon nasa na Japan ko Brazil ko kuma Faransa da ya mallaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.