Isa ga babban shafi
Coronavirus

India ta zama ta 3 a kasashen da ke da masu coronavirus fiye da miliyan

Kasar India ta zama ta uku da ke da adadin fiye da mutum miliyan guda da ke dauke da cutar coronavirus bayan Brazil da Amurka, dai dai lokacin da cutar ke ci gaba da yaduwa yayinda ake fargabar bullarta a karo na biyu a wasu sassan duniya.

Har yanzu Amurka ce kan gaba tukuna Brazil kana India a yawan masu dauke da cutar ta coronavirus.
Har yanzu Amurka ce kan gaba tukuna Brazil kana India a yawan masu dauke da cutar ta coronavirus. William WEST / AFP
Talla

Wannan cuta ta yi sanadin mutuwar fiye da mutane dubu dari 5 da 88, ta kuma harbi kusan miliyan 14 a fadin duniya tun bayan bullarta a yankin Wuhan na tsakiyar China cikin watan Disamban bara.

Duk da tsauraran matakan da aka dauka na takaita zirga zirgar jama’a da ya gurgunta tattalin arzikin duniya, annobar na ci gaba da ta’azzara a sassa da dama na duniya.

Adadin wadanda wannan cuta ta coronavirus ta harba a India ya zarce miliyan daya ne kwana guda bayan wadanda cutar ta kama a Brazil ya haura miliyan biyu.

Ita ma Amurka, a jiya Alhamis ta sanar da da dimbim mutane da suka harbu da wannan cuta, yayin da cutar ke ci gaba da zafafa gutsiri tsomar siyasa, inda kasashen yammacin Turai ke zargin Rasha da yunkurin satar bayanan binciken da ake na lalubo rigakafin cutar.

Duba da yadda mutane dari 6 ke mutuwa kullu yaumin a India a dalilin wannan cuta, hukumomin kasar sun sake killace miliyoyin mutane a sassan kasar, ta biyu mafi yawan al’umma a duniya.

A jiya Alhamis kafofin yada labarai a Birtaniya suka bayar da rahoton cewa wani gwajin da jami’ar Oxford ke yi na lalubo rigakafin wannan cuta ya nuna alamun sakamako mai armashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.