Isa ga babban shafi
Afghanistan

IS ta dau alhakin harin Kaboul

Manyan abubuwa masu fashewa da dama sun tarwatse a birnin Kaboul na kasar Afghanistan da sanyin safiyar yau Asabar.

Sojojin Afghanistan a birnin Kaboul
Sojojin Afghanistan a birnin Kaboul REUTERS/Omar Sobhani
Talla

Ya zuwa yanzu dai ba’a mutane 8 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon fashe-fashen, inda kamfanin dillancin labarai na AFP yace, anji kara mai karfin gaske a anguwannin Kaboul mafi cunkuson al’umma a tsakiya da arewaci.

Wannan na zuwa ne, yayin da Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ke ganawa da masu shiga tsakani na kungiyar Taliban da gwamnatin Afghanistan Asabar din nan, a wani alamun ci gaba a tattaunawar tasu yayin da Amurka ke hanzarta janye dakarunta daga kasar.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurkan, a yammacin Juma’a ta bayyana cewa, Pompeo zai yi ganawar ce, a lokuta daban-daban da bangaren gwamnatin Afghanistan da kuma kungiyar Taliban a kasar Qatar.

Pompeo zai kuma gana da sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani, da kuma Ministan Harkokin Wajen a Doha babban birnin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.