Isa ga babban shafi
Afghanistan

An soma tattaunawa tsakanin Taliban da Gwamnatin Afghanistan

An soma tattaunawa da mayakan kungiyar Taliban da gwamnatin Afghanistan aDoha na kasar Qatar, zaman da ake sa ran zai kai ga musayar fursunoni, da gawurtattun mayakan Taliban.

Mollah Abdul Ghani Baradar, Shugaban  talibans,  tareda Manzon amurka dangane da rikicin 'Afghanistan, Zalmay Khalilzad a Doha
Mollah Abdul Ghani Baradar, Shugaban talibans, tareda Manzon amurka dangane da rikicin 'Afghanistan, Zalmay Khalilzad a Doha REUTERS/Ibraheem al Omari
Talla

Nader Naderi kusa cikin zaman sulhun ya fadi a wani sakon tweeter cewa Bayan kokari sosai anyi katarin tsaida shawarar zaman sulhun tsakanin Gwamnatin Afghanistan da mayakan Taliban kuma tuni sun tashi daga inda suke zuwa inda za ayi wannan taro a yau.

Shugaban Amurka Donald Trump dai ya dauki wannan ganawa a matsayin daya daga cikin nasarorinsa ta fannin harkokin kasashen waje.

Bayanai na cewa Sakataren waje na Amurka Mike Pompeo da ya isa Doha na sa ran za a kawo karshen tankiyar a wannan zama.

‘Yan kasar ta Taliban nada yakinin cewa fara tattaunawan sulhu zai maido da zaman lafiya a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.