Isa ga babban shafi
Afghanistan

Yan Taliban sun kashe jami'an tsaron Afghanistan kusan 400

Gwamnatin Afghanistan tace akalla jami’an tsaron ta sama da 400 kungiyar Taliban ta kashe ko kuma ta jikkata a mako guda da ya gabata, abinda ke dada jefa shakku kan aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin bangarorin biyu.

Wasu daga cikin mayakan Taliban dake tsare
Wasu daga cikin mayakan Taliban dake tsare WAKIL KOHSAR / AFP
Talla

Ma’aikatar cikin gidan Afghanistan ta sanar da wadannan alkaluma inda take cewa yayin da tashin hankali ke raguwa a kasar tun bayan da kungiyar Taliban ta sanar da tsagaita wuta ranar 24 ga watan Mayu domin gudanar da Sallar Eid el Fitr, mayakan kungiyar na cigaba da kai hare hare kan jami’an tsaro.

Tareq Arian, mai Magana da yawun ma’aikatar yace a makon jiya kungiyar Taliban ta kai hare hare har sau 222 akan jami’an tsaron gwamnati, abinda yayi sanadiyar kashewa da kuma jikkata sojoji da yan sanda 422.

Jami’in ya kuma zargi kungiyar da kai hari kan shugabannin addini domin ganin sun sanya kiyayyar jama’a akan gwamnati wajen tada bam a Masallachin juma’a.

Arian ya zargi kungiyar da zama lemar kungioyoyin Yan ta’adda dake kai hari kan jama’a baji ba gani.

Shugaban kasa Ashraf Ghani ya sha alwashin cigaba da aiwatar da yarjejeniyar musayar firsinoni da kungiyar Taliban duk da karuwar hare haren da ake samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.