Isa ga babban shafi

Za'a saki mayakan Taliban dubu 5 a Afghanistan

Shugaban Kasar Afghanistan Ashraf Ghani ya bayyana shirin sakin mayakan Kungiyar Taliban dubu 5 da ake tsare da su a gidajen yarin kasar daga wannan makon, muddin kungiyar ta rage kai hare hare.

Mohammad Abbas wakilin kungiyar Taliban a shirin tattaunawar zaman lafiya da Amurka da Afghanistanvrier
Mohammad Abbas wakilin kungiyar Taliban a shirin tattaunawar zaman lafiya da Amurka da Afghanistanvrier REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Sanarwar daukar wannan mataki na zuwa ne sa’o'i bayan dakarun Amurka sun fara janyewa daga cikin kasar daga sansanoni biyu da aka girke su kamar yadda yarjejeniyar da suka kulla da Taliban ta tanada.

Mai Magana da yawun kungiyar Taliban Sediq Sediqqi yace daga ranar Asabar mai zuwa gwamnatin zata fara sakin kashin farko na mayakan kungiyar Taliban 1,500 domin tabbatar da aniyar ta na aiwatar da shirin, yayin da zata saki sauran 3,500 da zaran an fara tattauna wa tsakanin wakilan ta da na kungiyar.

A farkon watan nan Kungiyar Taliban ta kaddamar da hari kan sansanin sojin gwamnati, sa’oi bayan kawo karshen takaita bude wutar da ta yi, matakin da akayi tsammanin zai rusa yarjejeniyar zaman lafiyar da ta kulla da kasar Amurka.

Wani jami’in Ma’aikatar Tsaron Kasar ya ce, Taliban ta kai hare-hare akan sojojin gwamnati a yankuna 13 daga cikin 34 da ake da su, wanda ya hallaka soji 2.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.