Isa ga babban shafi
Amurka-Afghanistan

Amurka ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar Taliban

Bayan kwashe kusan shekaru 20 suna tafka yaki ba tare da samun nasara ba, yau kasar Amurka ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar Taliban dake Afghanistan wanda zai kai ga janye dakarun ta dake kasar.

Yarjejeniyar cimma sulhu tsakanin Amurka da yan kungiyar Taliban
Yarjejeniyar cimma sulhu tsakanin Amurka da yan kungiyar Taliban RFI
Talla

Jakadan Amurka Zalmay Khalizad ya sanya hannu a madadin kasar sa, yayin da Mullah Abdul Ghani Baradar ya sanya a madadin kungiyar Taliban.

A karkashin yarjejeniyar da bangarorin biyu suka sanyawa hannu a bikin da akayi a Doha, kasar Amurka zata janye sojojin ta dake Afghanistan a cikin watanni 14 masu zuwa, yayin da kungiyar Taliban zata daina kai hare hare da kuma tashin hankali.

Yayin bikin, Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bukaci kungiyar Taliban da ta yanke duk wata hulda da kungiyar Al Qaeda kamar yadda tayi alkawari, yayin da Sakataren tsaron Amurka Mike Esper ya ce suna iya watsi da yarjejeniyar muddin kungiyar Taliban taki mutunta ta wajen tattaunawa da gwamnatin Afghanistan da kuma daina kai hare hare.

A karkashin wannan yarjejeniya, bangarorin biyu, wato Amurka da Taliban za suyi musayar dubban firsinonin da suke tsare da su.

Kafin sanya hannu, shugaba Donald Trump ya bukaci al’ummar kasar Afghanistan da su rungumin sabon shirin wanda ake saran ya kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe shekaru 18 ana fafatawa a kasar.

Trump yace idan gwamnatin Afghanistan da kungiyar Taliban suka cika alkawarin da suka dauka, za su samu hanyar kawo karshen yakin dake gudana a kasar da kuma mayar da dakarun su zuwa gida.

Akalla sojojin Amurka 2,400 suka mutu a yakin na Afghanistan tun bayan mamaye ta da tayi a shekarar 2001, yayin da yanzu haka take da sojoji 12,000 a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.