Taliban ta kashe 'Yan sandan Afghanistan 13 a shingen binciken ababen hawa
Mayakan Kungiyar Taliban sun kai hari kan jami’an tsaron Afghanistan da ke aiki a wurin binciken ababan hawa inda suka kashe 13 daga cikin su.
Wallafawa ranar:
Mai magana da yawun 'yan Sandan Pule Khumri da ke yankin Baghlan, Ahmad Jawed Basharat ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce bayan wadanda suka mutu, wasu jami’an guda 5 kuma sun samu raunuka abinda ya sa aka ruga da su zuwa asibiti.
A wani labari kuma, jami’an tsaro guda 5 da mayakan Taliban 17 sun mutu sakamakon fafatawar da suka yi a tsakanin su a Yankin Uruzgan.
Hare-haren dai na zuwa dai dai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar sulhu tsakanin wakilcin kungiyar ta Taliban da gwamnatin kasar, tattaunawar da ke gudana a Qatar kuma ake gab da cimma jituwa don kawo karshen yakin kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu