Isa ga babban shafi
India-Coronavirus

Cutar COVID -19 ta kama sama da mutane miliyan 10 a India

Adadin wadanda suka kamu da cutar Coronavirus a India sun zarta miliyan 10 a yau Asabar, kamar yadda alkalumma na hukuma suka nuna, lamarin da ya maishe ta kasa ta 2 da cutar ta fi kamari, sai dai adadin sabbin kamuwa na raguwa ainun.

Ma'iakatan lafiya da ke jinyar masu Korona a babban asibitin Rajiv Gandhi, India.
Ma'iakatan lafiya da ke jinyar masu Korona a babban asibitin Rajiv Gandhi, India. REUTERS/P. Ravikumar/File Photo
Talla

Wadandan ke kamuwa da cutar a baya bayan nan a kasar sun kai dubu 25 a cikin sa’o’i 24.

A watan Satumba, kasar mai yawan al’umma biliyan 1 da dubu dari 3 tana samun masu harbuwa da wannan cuta da suka kai mutum dubu dari a cikin sa’o’i 24, har tana neman zarta Amurka, kasar da ta fi shan radadin wannan cuta.

Mazauna babban birnin kasar, New Delhi sun shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, har yanzu hankalinsu a tashe yake, sai dais un fi samun natsuwa idan aka kwatanta a da yadda lamarin yake kafin yanzu.

India ta dage dokar takaita zirga zirga da ta sanya a kasar don dakile yaduwar cutar, duba da yadda matakin ke kawo mata koma baya a fannin tattalin arziki, sai dai yanzu wasu jihohi da yankuna sun maido da dokar don takaita yaduwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.