Isa ga babban shafi
Afghanistan-Taliban

Afganistan za ta koma teburin tattaunawa da Taliban

Wakilcin gwamnatin Afghanistan da na Taliban za su koma teburin tattaunawa bayan janyewar kowanne bangare biyo a baya-bayan nan sakamakon karuwar hare-haren da gwamnati ke zargin Taliban na da hannu.

Wakilcin kungiyar Taliban.
Wakilcin kungiyar Taliban. REUTERS/Ibraheem al Omari
Talla

Wata majiyar tsaro a kasar ta ce bangarorin biyu za su koma teburin sulhu bayan cimma jituwa kan hakan a cikin watan Disamba don kawo karshen yakin kasar da ke ci gaba da salwantar da rayukan jama’a.

Taliban ta shiga tattaunawa da gwamnatin Afghanistan ne cikin watan Satumban bara a Qatar watanni kalilan bayan kammala kulla yarjejeniya da Amurka, yarjejeniyar da za ta kai ga janye dakarun ketare daga kasar.

Mai Magana da yawun ma’aikatar kula da harkokin zaman Lafiya na Afghanistan Najia Anwari ya ce tattaunawar sulhun tsakanin gwamnati da Taliban wani batu ne mai cike da sarkakiya amma za ta ci gaba saboda mutunta bukatar al’ummar kasar da suka nemi hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.