Isa ga babban shafi
Afghanistan

Afghanistan za ta cigaba da tattaunawar sulhu da Taliban a Doha

Kungiyar Taliban za ta koma teburin tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin Afghanistan a birnin Doha na Qatar a watan gobe.

Wasu wakilan kungiyar Taliban da na gwamnatin Afghanistan yayin zangon farko na tattaunawar sulhu a Qatar
Wasu wakilan kungiyar Taliban da na gwamnatin Afghanistan yayin zangon farko na tattaunawar sulhu a Qatar AFP
Talla

Tattaunawar ta baya-bayan nan tsakanin bangarorin biyu ta fara ne daga ranar 12 ga watan Satumba a wani kasaitaccen Otel da ke birnin na Doha, amma aka dakatar da ita har zuwa ranar 5 ga watan Janairun sabuwar shekara mai kamawa.

Mai magana da yawun Majalisar Kolin Sulhu ta Afghanistan, Faraidoon Khwazoon, ya ce, za a ci gaba da zaman sulhun ne ganin yadda kasashen duniya da suka yi tayin daukar nauyin zaman, suka janye saboda fargabar annobar Covid-19.

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani, ya so gwamnatinsa ta ci gaba da zaman zagaye na biyu da Taliban a birnin Kabul.

A farkon wannan wata na Disamba, masu shiga tsakani daga bangarorin biyu suka tsayar da shawarar tafiya hutu bayan kwashe watanni suna gudanar da zafafan taruka tare da daga jijiyoyin wuya kan abubuwan da suke da banbancin ra’ayi a kansu.

Kodayake a yanzu, masu shiga tsakanin sun ce, a shirye suke su dora kan ajandodin farko da zarar sun koma zaman a ranar 5 ga watan na Janairu.

Wannan tattaunawa na zuwa ne bayan Taliban ta cimma yarjejeniya da Amurka kan janye dakarun kasashen ketare da ke cikin Afghanistan daga watan Mayu mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.