Yawan wadanda suka mutu a tagwayen hare-haren Afghanistan ya kai 56
Jami’an lafiya sun ce, yawan wadanda suka mutu a tagwayen hare-haren ta’addancin da a ranar talata, aka kaiwa birnin Kabul da yankin Nangahar a Afghanistan ya karu zuwa mutane 56.
Wallafawa ranar:
A talatar da gabata ne wasu mahara suka kutsa kai cikin wani asibiti a Kabul, baban birnin Afghanistan inda suka halaka mutane 24 ciki harda jarirai 2, kafin daga bisani jami’an tsaro suyi nasarar kashe ‘yan bindigar.
Har zuwa wannan lokaci kuma, babu wani ko wata kungiya da tayi ikirarin kai harin, sai dai shugaba Ashraf Ghani na zargin kungiyoyin Taliban da kuma ISIS.
A Nangahar dake gabashin kasar kuwa, dan kunar bakin wake ne ya tarwatsa damarar bam din dake jikinsa a tsakiyar mutanen dake halartar jana'izar wani babban jami’in dan sanda, tuni kuma kungiyar ISIS ta dauki alhakin harin da yayi sanadin halakar rayuka 32, gami da jikkata wasu 132.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu