Isa ga babban shafi
Covid-19

Korona:Tawagar masana daga Hukumar Lafiya ta Duniya ta isa Wuhan

Wata tawagar kwararru daga hukumar lafiya ta duniya ta sauka a birnin Wuhan na kasar China don gudanar da bincike kan asalin cutar coronavirus, fiye da shekara guda bayan bullarta, sai dai an hana mambobin tawagar biyu karasawa kasar daga Singapore, bayan da gwaji ya tabbatar sun harbu da cutar.

Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Tawagar kasa da kasar da ta kunshi masana kimiyya 13, ta sauka China don gudanar da aikin da ya yi ta samun tsaiko, kuma an dauki samfurin mambobinta don yi musu gwajin cutar Covid 19, kana aka garzaya da su wani otel, inda za a killace su na tsawon makonni biyu gabanin fara aikin nasu.

An dai fara gano wannan cutar ne a birnin Wuhan na kasar China a karshen shekarar 2019, kuma tun daga wannan lokaci ne ta bazu zuwa sassan duniya inda ta kashe kusan mutane miliyan 2 ya zuwa yanzu, tare da kama gwamman miliyoyi a duniya.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce samun tabbacin cewa kwayar cutar ta samo asali daga dabba abu ne mai matukar mahimanci don dakile aukuwar haka a nan gaba.

Amma duk da watannin da aka shafe ana tattaunawa tare da bayani a kan aikin da masanan za su gudanar, sai da hukumomin China suka hana su shiga kasar a watan da ya gabata, lamarin da ke nuni da sarkakiyar siyasar da ke tattare da asalin annobar, abin da ke janyo cece kuce a tsakanin kasashe.

Isar wannan tawaga ta masana China na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta samu mutum guda da cutar coronavirus ta kashe a karon farko cikin watanni 8.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.