Isa ga babban shafi

Saudiya za ta sake bude ofishin jakadancinta na Qatar

Ministan harkokin waje Saudiyya, Faisal bin Farhan ya ce kasarsa za ta sake bude ofishin jakadancinta a Qatar a matsayin wani bangare na yarjejeniyar maido da huldar diflomasiyya a tsakaninta da makwafciyarta don kawo karshen gutsiri tsoma da suka shafe shekaru 3 su na yi.

Mohammed bin Salman, Yeriman Saudiya mai jiran gado.
Mohammed bin Salman, Yeriman Saudiya mai jiran gado. Saudi Royal Palace/AFP/Archives Texte par : RFI Suivre
Talla

Ministan ya ce Saudiyya za ta maido da cikakkiyar hulda da Qatar kamar yadda kasashen 2 suka amince a tattaunawarsu ta farkon wannan wata, kuma a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa za a sake bude ofishin jakadancin Saudiyya a birnin Doha.

Ya kara da cewa babu wani abin da zai kawo tsaiko a game da aniyar tasu, sai dai watakila matsaloli da suka shafi zirga zirga.

A watan Yunin shekarar 2017, Saudi Arabia da abokanta, Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain suka kakaba wa Qatar takunkumin da suka hada da haramta mata shawagi a srarain samaniyarsu bisa zargin cewa tana taimaka wa kungiyoyin ‘yan ta’adda, da kuma abotan da take da Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.