Isa ga babban shafi
China-India

Dakarun India da China sun sake gwabza fada a yankin Himalaya

An gwabza fada tsakanin sojojin China da na Indiya a yankin tsaunukan Himalaya da ya raba iyakar kasashen, wabda suka shafe shekaru suna takaddama kan mallakarsa.

Sojojin India a kusa da manyan bindigoginsu na artillery a sansanin da suka kafa kafin a kusa da iyakarsu da China.
Sojojin India a kusa da manyan bindigoginsu na artillery a sansanin da suka kafa kafin a kusa da iyakarsu da China. REUTERS/Stringer
Talla

Rahotanni sun ce an yi kare jini biri jini yayin fadan da bangarorin biyu suka gwabza.

Sabon rikicin na India da China na zuwa ne watanni 6 bayan gwabzawar da dakarunsu suka yi, abinda ya yi sanadin mutuwar sojin Indiya 20, da na China da kawo yanzu ba a bayyana adadinsu ba.

Fadan na baya bayan nan a ranar Lahadi, ya auku ne a yankin Naku La, a jihar Sikkim, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Hukumomi sun ce wata tawagar sojin China ce ta yi yunkurin ketarawa zuwa yankin India na Naku La, wanda ya hade jihar Sikkim da yankin Tibet na China, amma aka maida ta baya da karfin tuwo.

Raba rana da dakarun China da Indiya suka yi a shekarar da ta gabata a Sikkam ne ya janyo zaman tankiya tsakanin kasashen 2 da suka fi yawan al’umma a duniya.

A watan Yuni shekarar 2020, dakarun bagarorin 2 sun far wa juna da hannu da kulake da sanduna a kwarin Galwan na yankin Ladakh.

China da Indiya, wadanda suka yi yakin kan iyaka a shekarar 1962, sun zargi juna a game da tashin hankalin, zalika dukkaninsu suka jibge dubban sojoji a yankunan iyakokin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.