Isa ga babban shafi
China-India

Sojin India 3 sun mutu a wata arangamar tsakaninsu da Sojin China

Rundunar Sojin India ta tabbatar da mutuwar dakarunta 3 baya ga jikkatar wasu da dama yayin wata arangamarsu da Sojinta China a kan iyakar kasashen biyu, batun da yak ara tsamin alakar da ke tsakaninsu tare da aiki da karin dakaru daga kowanne bangare.

Firaministan India Narendra Modi.
Firaministan India Narendra Modi. REUTERS/Altaf Hussain
Talla

Tsawon shekaru kenan ana fuskantar takun saka tsakanin kasashen biyu masu karfin nukiliya game da mallakar yankin mai fadin kilomita dubu 3 da 500, a tsakanin yankin Tibet na China da Ladakh na India, sai dai sai a wannan karon lamarin ya yi tsamari har ta kai ga rasa rayuka.

Sanarwar Rundunar Sojin Indian ta ke tabbatar da arangamar ta ce ansamu asarar rayuka daga dukkannin bangarorin biyu, matakin da ya tilasta mata aikewa da karin dakaru na musamman.

A nata bangaren Ma’aikatar harkokin wajen China ta bakin Ministanta Zhao Lijian da ke bayyana yadda lamarin ya faru, ta ce guda cikin Sojin Indian da ke kan iyaka ne ya tsallaka yankin Chinan tare da farmakar dakarunta.

Chinan ta sake nanata gargadinta ga India kan yadda dakarunta ke karya ka’idojin kula da kan iyakar inda ko ranar 9 watan Mayu aka samu jikkatar jami’ai da dama .

Bangarorin biyu dais un tabbatar da cewa ba a samu musayar harbi sai dai an gwabza da jiki tsakanin dakarun na kan iyaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.