Isa ga babban shafi
China

China ta aiwatar da hukuncin kisa a kan tsohon ma'aikacin banki da aka kama da rashawa

A jiya Juma’a China ta aiwatar da hukuncin kisa a kan wani tsohon ma’aikacin banki, kuma tsohon shugaban wani asusun zuba hannun jari, Lai Xiaomin, bayan da kotu ta same shi da laifin karbar toshiyar baki na fiye da Yuro miliyan 215.

Shugaba Xi Jinping na China.
Shugaba Xi Jinping na China. REUTERS/Thomas Peter
Talla

A farkon wannan watan na Janairu ne kotu ta yanke wa Mr. Lai hukuncin kisa. Kotun ta kuma same shi da laifin auren mace fiye da daya, abinda aka haramta a kasar.

Alkaliyar kotun ta zargi Lai da karbar cin hancin sama da Yuro miliyan 215, kuma yana kokarin karbar karin Yuro miliyan 13.

Ta kuma danganta shi da kwanciyar magirbi a kan kudin al’umma da ya kai Yuro miliyan 3 da dubu dari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.